Dakarun Guards Brigade na rundunar sojin Najeriya sun ceto Misis Adonkie, matar wani tsohon Birgediya Janar, Basil Adonkie, sa’o’i kaɗan bayan da aka yi garkuwa da ita daga gidanta da ke Abuja.Rundunar ta bayyana hakan ne a wani rahoto na musamman da ta miƙa wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ranar Laraba.
Rahoton ya ce an sace Misis Adonkie da misalin ƙarfe 10:30 na dare ranar 1 ga watan Satumba, lamarin da ya sa aka tura dakaru domin farautar masu garkuwar ta hanyar wani samame na haɗin gwiwa.
A cewar rahoton, dakarun rundunar da kuma Army Headquarters Garrison sun bi sawun masu garkuwar ta yankunan ACO Estate da Gosa, inda suka yi arangama da su.
Dakarun sun yi nasarar ceto matar a kusa da ƙauyen Angwan-Sabo, yayin da wata tawaga ta ci gaba da bin sawun masu garkuwar da suka tsere.
Da misalin ƙarfe 11:09 na safe ranar Laraba, dakarun Bataliya ta 176 ta Guards Brigade da Bataliya ta 197 ta Special Forces sun tare wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a garkuwar, a kusa da ƙauyen Gaube da ke Kuje Area Council.
Dakarun sun ƙwato bindigar AK-47 guda ɗaya da kuma gidan harsashi mai ɗauke da harsasai 19 masu girman 7.62mm Special daga hannun waɗanda ake zargin.
Rundunar Guards Brigade ta ce an haɗa matar da aka ceto da iyalanta, yayin da ake tsare da mutanen biyu da aka kama domin gudanar da bincike da tantance su.
Ta ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano tare da cafke sauran mambobin ƙungiyar masu garkuwa da mutane.
Rahoton ya ce dakarun sun ƙara tsaurara ayyukansu a yankin domin bin sawun miyagun laifin da suka tsere, yana mai cewa ƙwarin gwiwar dakarun da kuma ƙwarewarsu wajen gudanar da ayyukan yaƙi na nan daram.