Iran ta aike wa Amurka sabon gargaɗi game da rikicin baya-bayan nan da ya ɓarke tsakanin ɓangarorin biyu.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, sakataren majalisar tsaron ƙasar, Mohsen Rezaei ya ce yun ƙurin da Amurkan ke yi ba zai taimaka mata ba."Wannan yunƙurin da kuke yi cikin matsananciyar damuwa ba za su taimaka muku ku kuɓuta daga cikin wutar da kuka hura wa kanku ba. Nan gaba kaɗan za ku ga yadda sabuwar dabarar Iran a fagen yaƙi, diflomasiyya da kuma tinkarar wareta daga duniya za ta rusa tushen ƙarfinku."
Kalaman na Rezaei sun zo ne bayan mafi munin musayar hare-hare tsakanin ɓangarorin biyu a cikin makonnin baya-bayan nan.
A hare-haren da aka kai kwanan nan, dakarun Amurka sun kai farmaki kan wurare da ke gaɓar mashigar Hormuz da kuma gabashinsa, baya ga wasu yankuna a yammacin Iran da kudu maso yammaci da kuma kudancin ƙasar.
Ɗaya daga cikin hare-haren ya yi sanadiyyar mutuwar mutum huɗu tare da jikkata wasu 68 a wani bikin aure da aka gudanar a birnin Kohstak da ke lardin Hormuz.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya bayyana harin a matsayin "laifin yaƙi."
Iran ta ce ta mayar da martani ne ta hanyar kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a faɗin yankin, ciki har da waɗanda ke Jordan da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Kuwait da Bahrain, da kuma Erbil, babban birnin yankin Kurdawa mai cin gashin kansa a Iraƙi.