Gwamnatin Jihar Legas ta amince tare da fitar da haɗaɗɗen jadawalin karatu na shekarar 2026/2027 ga dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu. Jadawalin ya tanadi Litinin, 14 ga Satumba, 2026 a matsayin ranar da za a koma makaranta domin fara sabon zangon karatu.
Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare na jihar, Jamiu Alli-Balogun, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis.
Ya ce an tsara jadawalin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi, wadda Ofishin Tabbatar da Ingancin Ilimi (Office of Education Quality Assurance) ya jagoranta.
Sanarwar ta ce kwamishinan ya bayyana cewa an kammala jadawalin ne bayan gudanar da taruka biyu da masu ruwa da tsaki, inda aka duba tare da amincewa da muhimman ranakun sabon zangon karatu.
Bisa ga jadawalin da aka amince da shi, zangon farko zai fara ne daga Litinin, 14 ga Satumba, 2026, zuwa Litinin, 21 ga Disamba, 2026, tare da hutun tsakiyar zango daga 2 zuwa 6 ga Nuwamba, 2026.
Zangon karatu na biyu zai fara daga 11 ga Janairu, 2027, zuwa 9 ga Afrilu, 2027, yayin da zangon karatu na uku zai gudana daga 3 ga Mayu zuwa 30 ga Yuli, 2027. Jimillar kwanakin karatu na shekarar za su kasance kwanaki 182.
Sanarwar ta ƙara da cewa Alli-Balogun ya bayyana haɗaɗɗen jadawalin a matsayin wata alama ta ƙudirin gwamnatin jihar na inganta ingancin ilimi da tabbatar da tsarin karatu mai kyau da tsari. Haka kuma ya buƙaci dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu su bi jadawalin da aka amince da shi ba tare da saɓawa ba.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa ana bikin Ranar Ilimi da Karatu ta Duniya (International Literacy Day) a ranar 8 ga Satumba, yayin da ake bikin Ranar Ilimi ta Duniya (International Day of Education) a ranar 24 ga Janairu.
Jadawalin ya kuma nuna cewa an bai wa makarantu damar zaɓar kowanne kwanaki biyu tsakanin Litinin, 7 ga Satumba, zuwa Juma'a, 11 ga Satumba, 2026, domin horas da ma'aikatansu don ƙara ƙwarewa, inda kowace makaranta za ta zaɓi lokacin da ya dace da ita.
Haka kuma, jadawalin ya tanadi cewa gudanar da Ranar Buɗe Makaranta (Open Day) wajibi ne ga dukkan makarantu, duk da cewa kowace makaranta za ta iya zaɓar ranar gudanar da ita. Sannan dukkan ranakun hutun gwamnati wajibi ne a kiyaye su, kuma za su kasance ƙarƙashin duk wani sauyi da Gwamnatin Tarayya ta sanar.