Tarihin rayuwar wata fitacciyar baƙar fata da ta kafa tarihi a fannonin ƙirar kayan sawa da shari’a da diflomasiyya a matakin duniya, na ci gaba da zama gagarumin darasi ga al'umma game da yadda lokaci da tsufa ke sauya matsayin ɗan Adam.
Gimbiya Elizabeth Bagaaya (wadda aka fi sani da Princess Elizabeth of Toro), an haife ta a shekarar 1936 a matsayin Gimbiya a Masarautar Toro da ke Uganda (ɗiya ga Sarki Rukidi III). Ta karanci Shari’a a Jami’ar Cambridge (Girton College) a Birtaniya, inda a shekarar 1965 ta zama mace ta farko daga Gabashin Afirka da ta kafa tarihin zama lauya a Birtaniya (English Bar).
A shekarun baya, ta kafa tarihi a matsayin ɗaya daga cikin baƙaƙen mata na farko da suka samu damar yin aiki da shahararriyar hukumar ƙirar kayan sawa ta Ford Agency a ƙasar Amurka.
Kyawunta da fasaharta sun sa shahararrun mujallu na duniya irin su Harper’s Bazaar da Vogue sun wallafa hotunanta tare da ware mata shafuka na musamman.
Bayan nasarorinta a fannin ƙirar kayan sawa, ta ƙara faɗaɗa iliminta inda ta karanta shari’a a Jami’ar Cambridge da ke ƙasar Ingila, har ta zama gogaggiyar lauya. Daga bisani ta shiga fannin gwamnati da diflomasiyya, inda ta riƙe manyan muƙamai na harkokin ƙasashen waje tare da gudanar da ayyukan diflomasiyya a matakin ƙasa da ƙasa.
A ɓangaren rayuwar iyali, ta auri wani ƙwararren injiniyan jiragen sama a birnin Landan, wanda ke da alaƙa da gidan sarautar Wilberforce Nyabongo.
Sai dai a yanzu, bayan tsawon shekaru ana tafiya da ita a fagen duniya, sauyin lokaci ya bayyana sarai a tare da ita. Bayan haura shekaru 90 a duniya, ta koma ƙasarta ta haihuwa, Uganda, inda take gudanar da rayuwarta cikin tsufa.
Tsufa ya bayyana a jikinta: gashinta ya yi fari sarai, fatar jikinta ta sauya, sannan ƙarfin jiki da kyan fuskar da ta shahara da su a baya duk sun zama tarihi.
Masana da masu lura da al’amuran yau da kullum na kallon sauyin rayuwarta a matsayin babban alamar tunatarwa cewa ɗaukakar duniya ba mai dawwama ba ce.
Labarinta yana isar da saƙo guda ga bil adama, kyau, ƙuruciya, da matsayi abu ne mai shuɗewa, saboda haka tanadin kyakkyawan aiki, tsoron Allah, da neman abin da zai amfana bayan rabuwa da duniya shi ne mafi muhimmanci.
Tags
Labarai