Tsohon Ministan Wasanni kuma lauya, Solomon Dalung, ya buƙaci Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, da ya gabatar da ƙwararan hujjoji kan zargin da ya yi cewa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya shirya kashe-kashen jama’a tare da biyan ’yan bindiga kuɗi a lokacin mulkinsa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Dalung ya bayyana cewa kalaman na Ministan Tsaro sun wuce batun sa-in-sa ta siyasa kawai tsakanin fitattun ’yan Arewa biyu. A cewarsa, wannan babban zargi ne na aikata laifi mai nauyin da ke buƙatar cikakken bincike na doka da gabatar da shaidu maimakon dogaro da kalaman kafafen yaɗa labarai.
Dalung ya karkata hankali kan kalaman Janar Musa na cewa: "Ba za mu taɓa jin daɗin mutumin da da gangan ya shirya kashe mutanenmu ba." Ya jaddada cewa tunda irin wannan magana ta fito daga bakin Ministan Tsaro mai ci wanda kuma ya taɓa zama Babban Hafsan Tsaron Ƙasa (CDS) ya zama wajibi a buɗe fayiloli da rahotannin sirri domin tabbatar da gaskiyar lamarin.
Tsohon ministan ya tunatar da cewa rikicin ƙabilanci da addini a Jihar Kaduna bai fara a shekarar 2015 lokacin da El-Rufai ya zama gwamna ba. Ya kafa hujja da rahotannin tsohon Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Janar Martin Luther Agwai, waɗanda suka fito da tarihin rikice-rikicen shekarun 1987 (Kafanchan), 1992 (Zangon Kataf), 2000 (Shari'a), da kuma rikicin bayan zaɓen 2011.
Ya bayyana cewa duk da cewa El-Rufai yana da tambayoyin da ya kamata ya amsa a kan yadda ya gudanar da mulkinsa daga 2015 zuwa 2023, akwai bambanci babba tsakanin cewa gwamnatinsa ta gaza wajen kare jama'a da kuma cewa da gangan ya shirya kashe mutane.
Game da batun kuɗaɗen da El-Rufai ya taɓa amsa cewa gwamnatinsa ta biya. Dalung ya buƙaci Janar Musa da ya fayyace ko kuɗin da aka biya a matsayin diyya ta sulhu bayan rikicin 2011 ne, ko kuma 'yan bindiga aka biya kai tsaye.
Ya kuma ambaci matsayin tsohon GOC na Runduna ta 1, Manjo-Janar Danjuma Ali-Keffi (mai ritaya), wanda ya ƙalubalanci Janar Musa yana mai cewa a lokacin da yake komandansa, El-Rufai bai taɓa ba da umarnin dakatar da ayyukan soja kan masu aikata laifuka ba.
A matsayinsa na tsohon jami'in soja mai muƙami na sama, Dalung ya jefa tambayoyi zuwa ga Janar Musa game da abin da hukumomin tsaro suka sani a lokacin mulkin El-Rufai:
Shin akwai rahotannin sirri da aka gudanar a lokacin?
Shin an mika rahotannin ga Shugaban Ƙasa ko Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro?
Idan an kai rahoton aka ƙi ɗaukar mataki, me ya sa ba a sanar da 'yan Najeriya ba sai yanzu?
Dalung ya kuma taɓa batun rarrabuwar kawuna sakamakon zaɓen mataimaki Musulmi da El-Rufai ya yi a Kaduna. Ya bayyana cewa idan har ana kallon tikitin Musulmi da Musulmi a matsayin hatsari ga haɗin kan jama'a, to dole ne a kalli gwamnatin tarayya ta yanzu ƙarƙashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima da irin wannan madubin.
A ƙarshe, Dalung ya jaddada cewa rubutunsa bai yi shi domin wanke El-Rufai ba, amma saboda muhimmancin zaman lafiya da adalci ga al'ummar Kudancin Kaduna da aka daɗe ana cutarwa. Ya buƙaci Ministan Tsaro da ya miƙa duk wata hujja ga hukumomin shari'a domin gudanar da bincike na adalci, domin hana maida muhimman batutuwan tsaron ƙasa makamin siyasa.