A wani babban mataki na tsare hanyoyin dogaro da kai na manoma daga ƙalubalen yanayi, Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙaddamar da aikin 'Kare Tsaron Abinci Daga Ambaliyar Ruwa da Fari' na dalar Amurka miliyan 1.
Wannan shiri na da nufin ƙarfafa al'ummomin manoma domin jure tasirin ambaliyar ruwa da fari, tare da tabbatar da ɗorewar haɓakar tattalin arziƙi da abinci a faɗin jihar bakiɗaya.
Bayanan da ya kamata Ku sani game da maƙasudin shirin sun haɗa da:
1. Tallafi da Aiwatarwa: Ƙungiyar Mercy Corps Nigeria ce ke aiwatar da aikin tare da haɗin gwiwar Hukumar Gudanar da Ci gaban Jihar Katsina (KTDMB) da Ma'aikatar Kasafin Kuɗi da Tsarin Tattalin Arziƙi.
2. Yankuna na Farko: Yankunan da za su fara sharɓar domin shirin sun haɗa da: Karamar Hukumar Bindawa da Bakori da kuma Kafur.
3. Masu Amfana: Waɗanda za su amfani da shirin su ne: Manoma masu ƙaramin karfi da mata, matasa, da kuma magidanta masu rauni.
Mabuɗan Ayyuka:
1. Gyaran Ƙasa da Tafiyar da Ruwa: Gyara ƙasar noma da inganta magudanan ruwa, da gyaran cibiyoyin ruwa masu amfani da hasken rana.
2. Rage Asara Bayan an Yi Girbi: Inganta tsarin adana abinci a rumbuna domin rage lalacewar amfanin gona.
3. Noma Wanda Ya Dace da Yanayi: Horar da manoma kan dabarun noma na zamani da faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga.
Gwamnatin jihar ta jaddada cewa tsaron abinci shi ne ginshiƙin ci gaban kowace al'umma, musamman a Katsina inda noma shi ne babban tsarin rayuwar jama'a.
An miƙa kundin dokoki da umarni ga ma'aikatun da abin ya shafa domin tabbatar da gudanarwa da sanya ido wajen aiwatar da shirin.