Gasar Rubutacciyar Wakar Hausa TA Ranar Marubutan Hausa Ta Duniya 2026

KWAMITIN SHIRYA TARON RANAR MARUBUTA HAUSA HADIN GUIWA DA MAIGEMU DEVELOPMENT FOUNDATION

GASAR RUBUTACCIYAR WAƘAR HAUSA TA RANAR MARUBUTAN HAUSA TA DUNIYA 2026

Cikin shirye-shiryen bukin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya na shekarar 2026 wanda za a gabatar a Birnin Katsina a ranakun 31/12/2026 zuwa 01/01/2027. Akwai gasar rubutacciyar waƙar Hausa a kan batun Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi. 

Kowa yana da damar shiga gasar, daga marubuta maza da mata sanannu da sababbi da ma masu sha'awar fara rubutun waƙa, matuƙar za su kiyaye ƙa'idojin gasar. 

MAUDU'IN GASAR

Yaƙi da sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi

MANUFOFIN GASAR

1. Ƙarfafa marubuta su yi nazari kan yadda tu'ammali da miyagun ƙwayoyi ke shafar goben ƙasarmu tare da haska dabaru na yaƙi da matsalar. 

2. Samar da sababbin ra’ayoyi da mafita na zamani da za su iya taimaka wa al’umma wajen fuskantar ƙalubalen sha da fataucin miyagun ƙwayoyi. 

3. Sake fito da wata kafa ta musayar ra’ayi kan alaƙar shaye-shaye da safarar miyagun ƙwayoyi da taɓarɓarewar tarbiyyar al'umma. 

4. Ba wa marubuta damar nuna fasaha da basira da ƙwarewarsu a fannin rubutu da bincike ko ƙirƙira, musamman a kan abin da ya shafi tu'ammali da miyagun ƙwayoyi. 

5. Samar da ƙarin abin karatu mai inganci da manufa cikin harshen Hausa. 

TSARE-TSAREN SHIGA GASAR

1. Za a aiko da rubutacciyar waƙa mai ƙwar biyu, wadda ba ta gaza kuma ba ta wuce baiti 20 ba, ta wannan adireshin; ranarmarubutanhausa2025@gmail.com daga ranar 05/10/2026 zuwa ranar 30/10/2026. 

2. Za a zaɓi waƙoƙi 5 da suka ƙayatarwa, waɗanda marubutansu za su rera a ranar Taron kuma daga cikin biyar ɗin ne za a fitar da na ɗaya da na biyu da na uku a alƙalancin ƙarshe a Ranar Marubutan Hausa ta Duniya 2026. 

*SHARUƊƊAN SHIGA GASAR*

1. A tabbatar waƙar ta dace da batutuwan da suka shafi yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi. 
2. Dole ne a bi tsarin amsa-amo na ciki da na waje(amma kowane marubuci yana da zaɓin nasa). 
3. A tabbatar an yi amfani da daidaitacciyar Hausa kuma an kiyaye ƙa'idojin rubutun Hausa.Dole ne amfani da haruffa masu lanƙwasa(ɓ, ɗ, ƙ, 'y).
4. A tabbatar an aiko da waƙar a tsarin Microsoft word kawai zuwa ga wannan email ɗin; ranarmarubutanhausa2025@gmail.com. tare da shedar yin rijista.
5. A tabbatar ba a taɓa shiga wata gasa da waƙar da za a turo ba, kuma ba a taɓa bugawa a jarida ko wata kafa ko zaurukan kafafen sadarwa na zamani ba.
6. Wanda ya yi rijista da taron Ranar Marubuta Hausa ta 2026 ne kaɗai zai iya shiga gasar.
7. Kada waƙar ta zamto ta ci zarafi ko tozarta wata al'umma ko ɗaiɗaikun mutane.
9. A sani, hukunci da sakamakon alƙalan gasar shi ne na ƙarshe, ba za a sake tattauna shi ba a wani waje.
11. Kowane marubucin waƙa yana iya shiga gasar ban da mambobin kwamitin ƙoli na shirya wannan taro.

KYAUTUTTUKAN DA GASAR ZA TA SAMAR 

1. Za a bayar da kyaututtuka ga labarai uku da suka yi zarra a matakin na 1 zuwa na 3. 

2. Za a bayar da takardar shaidar karramawa da awalaja ga waɗanda suka shiga gasar daga na 1 zuwa na 15 kuma za a duba yiwuwar buga waƙoƙin nasu cikin littafin da za a ƙaddamar da shi a taron shekara mai zuwa ta 2027. 

Dr. Mujaheed Abdullahi Kudan,
A madadin Kwamitin Shirya Gasa na Ranar Marubutan Hausa 2026.

Post a Comment

Previous Post Next Post