Kasafin kuɗin Asusun Tallafa wa Ilimin Manyan Makarantu (TETFund) ya karu sosai daga naira biliyan 320.3 a shekarar 2023 zuwa naira tiriliyan 1.6 a shekarar 2025, lamarin da ke nuna ƙarin zuba jari da gwamnatin tarayya ke yi a fannin ilimin manyan makarantu.Shugaban Kwamitin Amintattu na TETFund, Aminu Bello Masari, ne ya bayyana hakan a taron tattaunawa da al’umma na ƙasa na shekarar 2026 da asusun ya gudanar a Abuja a jiya.
Masari ya ce kuɗaɗen asusun sun tashi daga naira biliyan 320.3 a shekarar 2023 zuwa naira biliyan 683.4 a shekarar 2024, kafin su kai naira tiriliyan 1.6 a shekarar 2025. Wannan adadi ya kai kusan ninki biyar na kuɗin da aka ware a shekarar 2023, abin da ke nuna jajircewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen bunƙasa ƙwarewar al’umma.
Sai dai ya jaddada cewa dole ne ƙarin kuɗaɗen ya haifar da sakamako na zahiri wajen inganta ƙwazon ɗalibai, bunƙasa ayyukan bincike da kuma ƙara wa waɗanda suka kammala karatu damar samun aikin yi.
Masari ya bayyana cewa manyan makarantu 271 ne za su amfana da tallafin kai tsaye na shekara-shekara na shekarar 2026. Ya ce kowace jami’a za ta samu kusan naira biliyan 2.526, kowace kwalejin kimiyya da fasaha (polytechnic) za ta samu naira biliyan 1.871, yayin da kowace kwalejin ilimi (College of Education) za ta samu naira biliyan 2.057.
Ya ce TETFund ya ware naira biliyan 10 a shekarar 2026 domin cibiyoyin koyon sana’o’i a kwalejojin kimiyya da fasaha. Haka kuma, asusun ya tallafa wa cibiyoyin ƙirƙire-ƙirƙire da bunƙasa kasuwanci a jami’o’i 12, tare da amincewa da naira biliyan 48 domin inganta kayan aiki da cibiyoyin koyar da injiniyanci da fasaha.
Ya ƙara da cewa an amince da naira biliyan 6.09 domin tallafa wa ayyukan bincike guda 174 da suka yi nasara a zagayen bayar da tallafin Asusun Bincike na Ƙasa na shekarar 2025.
Haka kuma, ya bayyana cewa shugaban ƙasa ya amince da kafa ƙarin cibiyoyin ƙwarewa guda shida da za su mayar da hankali kan fasahar mutum-mutumi (robotics), rubuta shirye-shiryen kwamfuta (coding), basirar wucin gadi (Artificial Intelligence), koyon na’ura (machine learning) da tsaron yanar gizo (cybersecurity). Wannan ya kai jimillar cibiyoyin ƙwarewa da ke ƙarƙashin shirin zuwa 36.
Masari ya buƙaci cibiyoyin da ke amfana da tallafin da su tabbatar da gaskiya da riƙon amana, sarrafa kuɗaɗen yadda ya kamata da kuma kula da kayayyakin more rayuwa. Ya gargaɗi cewa samar da kuɗaɗe kaɗai ba zai magance dukkan matsalolin da fannin ilimi ke fuskanta ba.
A nasa jawabin, Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya ce gwamnati na yin garambawul ga manhajojin karatu domin samar da waɗanda suka kammala karatu da ƙwarewar aiki da ta dace da buƙatun masana’antu.
Alausa ya yaba wa TETFund bisa tallafa wa ayyukan more rayuwa, bincike da samar da na’urori na musamman a manyan makarantu.
Ya ce daga cikin sauye-sauyen da ake shirin aiwatarwa akwai tsarin manhajar karatu da zai mayar da kashi 80 cikin 100 na koyarwa kan aikace-aikace, yayin da kashi 20 cikin 100 za su kasance na koyarwar ka’ida.
Ya kuma bayyana cewa an samar da sabbin manhajojin difloma na ƙasa guda 36 tare da sake duba wasu daga cikinsu, da ƙarin shirye-shiryen difloma na ƙasa guda 10, da takardun shaidar ilimi na ƙasa guda 30, da kuma ƙa’idojin sana’o’i na ƙasa guda 21. Bugu da ƙari, an samar da wasu sababbi guda 27 tare da sake duba guda huɗu.
Alausa ya ce za a ci gaba da daidaita shirye-shiryen karatu da buƙatun kasuwar aiki. Ya ƙara da cewa shirye-shirye irin su Asusun Lamunin Ilimi na Ƙasa (NELFUND) za su faɗaɗa damar samun ilimi, ta yadda matsalar kuɗi, nakasa ko wurin zama ba za su hana ’yan Najeriya da suka cancanta kammala karatunsu ba.
A nasa ɓangaren, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya bayyana ilimi a matsayin muhimmin ginshiƙi wajen bunƙasa ƙwarewar al’umma da haɓaka ayyukan tattalin arzikin ƙasa.
Akume ya yi kira da a ƙarfafa sa ido kan ayyukan da ake gudanarwa da kuma bayar da rahotanni cikin gaskiya, domin tabbatar da cewa zuba jarin da ake yi a fannin ilimi yana haifar da sakamako mai amfani.
Shi kuwa Babban Sakataren TETFund, Sonny Echono, ya bayyana cewa an kammala ayyuka sama da 418 a manyan makarantun da ke amfana da tallafin asusun, kuma suna shirye domin buɗe su a hukumance. Ya ce akwai wata cibiya guda da aka kammala ayyuka 14 a cikinta.
Echono ya ce asusun na faɗaɗa zuba jarinsa a fannonin more rayuwa, bincike, jin daɗin ɗalibai, ƙirƙire-ƙirƙire da koyon zamani ta hanyar fasahar dijital.
Ya ƙara da cewa TETFund na tallafa wa ɗalibai wajen bunƙasa sabbin dabaru, tun daga ƙirƙirar ra’ayi har zuwa kare haƙƙin mallakar fasaha da samar musu da alaƙa da masana’antu.
Echono ya kuma bayyana cewa shirin samar da motocin sufuri ga ɗalibai ya shafi manyan makarantu 42. Ya ce an samar wa makarantu kusan 98 da motocin da ke amfani da wutar lantarki domin sauƙaƙa zirga-zirgar ɗalibai cikin araha.
Ya ƙara da cewa TETFund na aiki tare da Ma’aikatar Kwadago domin daidaita shirye-shiryen koyon sana’o’i da haɓaka ƙwarewa da buƙatun ma’aikata a ƙasar.