Kotu ta Umarci INEC ta yi wa Jam'iyyar Matasa Rajista

Kotun tarayya ta umurci INEC ta yi wa jam‘iyyar Access Party da ake kira da Jam'iyyar Matasa ta su Bulama Bukarti rajista.

Kafar yaɗa labarai ta BBC ta ruwaito cewa wata kotun tarayya wadda ke zamanta a Abuja ce ta bayar da wannan umurnin, sannan ta umarci INEC ta ba jam'iyyar damar ƙarasa rajistarta.

Jagororin jam'iyyar Dr. Audu Bulama-Bukarti da Mevon Samuel ne suka maka INEC a kotu a matsayin jam'iyyar, bayan hukumar mai zaman kanta ta ƙi amincewa da ita, inda ta kafa hujja da cewa tambarin jam'iyyar ya yi kama da tambarin wata jam'iyyar.

Da yake yanke hukunci, alƙalin kotun Mai shari'a Obiora Atuegwu Egwuatu na kotu a 11 ya ce hukumar ba ta da hurumin hakan, inda ya nanata cewa hukuncin ba daidai ba ne, kuma ya saɓa da shari'a kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 y tsara da kuma sashe na 79 na kundin zaɓe na 2022.

Post a Comment

Previous Post Next Post