Farashin man fetur na ci gaba da sauka a kasuwannin duniya bayan Amurka da Iran ta sanya hannu kan yarjejeniyar cikin daren da ya gabata.
Yarjejeniyar ta ƙunshi buɗe mashigar Hormuz, wadda ta kasance ɗaya daga cikin hanyoyin fitar da mai zuwa kasuwannin duniya.A farkon mako an riƙa sayar da gangar mai samfurin Brent kan dala 86.80, yayin da a yanzu ake sayar da shi kan dala 74.80