Rahotanni sun ce ’yan bindiga sun kashe Hakimin Gundumar Gallah, Alhaji Ahmed Yusuf, wani basarake da ke ƙarƙashin Masarautar Borgu a Jihar Neja, bayan zargin ya gargadi ’yan bindigar da su nisanci al’ummarsa.An ce an kai wa basaraken, wanda aka fi sani da Magajin Garin Gallah na Ƙaramar Hukumar Agwara, hari a fadarsa a ƙarshen makon da ya gabata.
A cewar rahotannin da jaridar The News Chronicle ta samu a ranar Talata, ’yan bindigar sun kai wa basaraken hari ne bayan zargin ya yi musu gargaɗi kan yunƙurinsu na kutsawa cikin al’ummar.
Mai sharhi kan harkokin tsaro, Bakatsine, ne ya fara bayyana labarin kisan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X.
Haka kuma, an ruwaito cewa Alhaji Ahmed Yusuf ɗan’uwa ne ga Ministan Ƙasa na Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, CON.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani kan yadda harin ya faru ba, ciki har da ainihin lokacin da aka kai harin da kuma ko akwai wasu mutanen da suka rasa rayukansu.
Ofishin Shugaban Ƙaramar Hukumar Borgu ya tabbatar da mutuwar hakimin, inda ya bayyana lamarin a matsayin “abin takaici matuƙa kuma mai tayar da hankali.”
Masarautar Borgu ita ma ta tabbatar da mutuwarsa a cikin wata sanarwa da Ibrahim Toriq Abubakar ya fitar ranar Lahadi, 23 ga Agusta, 2026.
Sanarwar ta ce: “Masarautar Borgu na alhinin rasuwar manyan ’ya’yanta biyu kuma ’ya’yan sarauta, Alhaji Garba Alhassan (Tafidan Borgu) da Alhaji Ahmed Yusuf (Magajin Garin Gallah).”
Masarautar ta bayyana rasuwarsu a matsayin babban rashi ga iyalansu, masarautar gargajiya da kuma al’ummar Borgu baki ɗaya.
Ta kuma mika ta’aziyyarta ga iyalan mamatan, ’yan’uwa, abokai da makusantansu, tare da roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta musu kurakuransu, Ya kuma ba su madawwamin hutu a Jannatul Firdaus.
Haka kuma, masarautar ta yi addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai da kariya mai ɗorewa a Masarautar Borgu, tare da roƙon Allah Ya ba iyalan mamatan ƙarfin jure wannan babban rashi.