Wane Ne Bahaushe? Ku Kasance Damu a Ranar 31/12/2025 Domin Sanin Waye Bahaushe

 Za mu kasance da Farfesa Mu’azu Sa’adu Muhammad a ranar 31/12/2025 a Dutse baban birnin jihar Jigawa domin sanin waye Bahaushe daga tushe.

Farfesa Mu’azu Sa’adu Muhammad

Farfesa Mu’azu Sa’adu Muhammad an haife shi a ranar 13 ga Maris, 1964, a Kudan, Jihar Kaduna, Najeriya. Ya fara karatu daga makarantar allo (1969–1972), firamare a Kudan (1973–1979), sakandare a GSS Kagoro da Maƙarfi (1979–1984), sannan I.J.M.B a Kwalejin Zurfafa Ilimi, Zariya (1985–1987). Ya samu digiri na farko (B.A Hausa, 1998), digiri na biyu (M.A Hausa, 2007), da Ph.D Hausa (2016) a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sokoto.

Ya fara aiki a Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Kaduna (1988–1995), Ma’aikatar Ilimi Kaduna (1995–2003), Kwalejin Sardauna Kaduna (2003–2010), sannan Jami’ar Sule Lamido, Kafin Hausa, Jigawa (2014–yanzu). An nada shi Farfesa a ranar 17 ga Nuwamba, 2025.

Farfesa Mu’azu ya wallafa littattafai da yawa, ƙasidu a mujallu na ƙasa da kasa, da kuma aikin fassara. Ya jagoranci dalibai a matakai daban-daban na B.A, M.A, da Ph.D a fannonin Adabi, da Al’adun Hausawa. Hakanan ya bayar da gudunmawa ga al’umma ta hanyar koyarwa da tarurrukan horo da ayyukan ci gaban al’umma.

Yana da aure da yara goma (10), kuma ya ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen ilmantarwa da raya al’adun Hausawa.


Post a Comment

Previous Post Next Post