Amurka Za Ta Soke Bizar Bakin Kasashen Waje Da Suka Nemi Mafaka Bayan Shiga Kasar

Gwamnatin Amurka ta ce tana shirin soke bizar wasu baƙin ƙasashen waje da suka shiga ƙasar domin yawon buɗe ido ko kasuwanci, amma daga baya suka nemi mafaka (asylum) domin su tsawaita zaman su a ƙasar.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ce ta bayyana hakan a ranar Talata, inda ta ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Donald Trump na rage yawan ƙaura zuwa Amurka.

Gwamnatin ta ce yanzu tana aiki tare da Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida wajen gano mutanen da suka shiga Amurka da sunan baƙuncin wucin gadi, amma daga baya suka nemi mafaka domin su samu damar zama a ƙasar na dindindin.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, Tommy Pigott, ya ce neman biza da nufin amfani da ita wajen neman mafaka yaudara ce, kuma hakan na daga cikin dalilan da za su iya sa a soke bizar.

Fadar White House ta bayyana a wani saƙo da ta wallafa a shafin X cewa wannan mataki na iya shafar biza har 200,000, inda ta kira shi “mafi girman soke biza a lokaci guda a tarihin Amurka.”

Sai dai Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ba ta tabbatar ko musanta wannan adadi ba. Pigott ya ce yawan bizar da za a soke har yanzu yana sauyawa, kuma za a riƙa soke su a hankali yayin da ake gano waɗanda abin ya shafa.

A farkon wannan watan, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce tun bayan da Shugaba Donald Trump ya koma kan karagar mulki a watan Janairun 2025, an soke bizar kusan baƙin ƙasashen waje 175,000 bisa dalilai daban-daban.

Dalilan sun haɗa da aikata laifuka, ciki har da tuƙi cikin maye, da kuma yabawa kisan wani ɗan rajin kare ra’ayin masu ra’ayin dama, Charlie Kirk.

Gwamnatin Amurka ta kuma soke bizar wasu jami’an Mexico, ciki har da ɗan tsohon shugaban ƙasar, Andrés Manuel López Obrador. Wannan mataki ya sa shugabar Mexico ta yanzu, Claudia Sheinbaum, ta gabatar da ƙorafi.

Trump, wanda ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasar ne a babban ɓangare saboda alƙawarinsa na yaƙi da ƙaura ba bisa ƙa’ida ba, ya kori adadi mai yawa na mutanen da ke Amurka ba tare da takardun izinin zama na doka ba.

Sai dai gwamnatin tasa ta kuma ƙara tsaurara matakan hana wasu baƙin ƙasashen waje shiga Amurka, tare da ɗaukar mataki kan waɗanda suka ci gaba da zama a ƙasar bayan ƙarewar bizar da aka ba su.

Wasu daga cikin waɗannan matakai sun fuskanci ƙalubale a kotuna, inda aka dakatar ko rage tasirinsu.

A ranar Juma’a da ta gabata, wani alkalin gwamnatin tarayya ya soke dokar da gwamnatin Amurka ta kafa wadda ta hana bayar da biza ga ‘yan ƙasashe 75 da ke son zuwa Amurka domin zama na dindindin.

Daga cikin ƙasashen da dokar ta shafa akwai Afghanistan, Brazil, Masar, Iran, Iraq, Najeriya, Somalia, Thailand da Yemen.

Gwamnatin Trump ta kuma ce tana shirin ƙara tsaurara binciken shafukan sada zumunta na mutanen da ke neman bizar Amurka.

Pigott ya ce gwamnati tana ƙara jaddada cewa, “Biza gata ce, ba haƙƙi ba.”

Post a Comment

Previous Post Next Post