A wasanni goman farko da aka fara fafatawa ba gasar cin kofin Premier League na Ingila, Ƙungiyar Jajayen Aljanu (Manchester United) ce kaɗai aka yi fashin maku uku da bashin ƙwallaye biyu a cikin manyan ƙungiyoyin gasar.
A wasan da aka fara ranar Juma'ar wanda ƙunguyar Arsenal ta buɗe wasan, ta lallasa abokiyar Karawarta Coventry da vi 3 da nema 0 wanda hakan ya ba su damar ɗarewa saman teburin gasar tun a ranar farko.
Sai kuma ranar Asabar Hull City ta kama Manchester United ta yi mata luguden ƙwallaye biyu, bayan da magoya bayan Manchester United ɗin suka gama cika baki a kan cewa, yau za su hau teburi, sai ga su ana hango su a matakin na 19.
Bayan wasan Manchester United sai ƙungiyar ƙwallon Brighton ta rikirkito da Arsenal ƙasa inda suka dawo na biyu, yayin da Brighton ta Hayes kan karagar teburin a matsayin ta 1, bayan da ta doke ƙungiyar Aston Villa da vi 4 da nema 0, wasan da ya girgiza dukkan masu kallon gasar ta premier League duba da irin yadda ƙunguyar ta Aston Villa ta hasta a kakar wasan da ya shuɗe.
Daga ƙarshe dai Manchester City ta samu da ƙyar ta ƙwaci kanta a hannun Bournemouth da vi 2 da 1. Yayin da Liverpool ta yi canjaras da Newcastle United 2 da 2. Sai kuma Chelsea da ta rufe wasan makon a ranar Litinin inda ita ma ta ƙwaci maki 3 da ƙyar a hannun Fulham a wasan da aka tashi 2 da 1.
Wannan ya ba wa Brighton zamowa ma 1 a saman teburin yayin da Arsenal le matsayin na biyu, sai kuma Brentford a matakin na 3. Sai kuma ƙungiyoyin Coventry da Tottenham da kuma Aston Villa da suke a matakin na 18 da 19 da kuma na 20 a wasan farko na gasar ta Premier League.