A wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa, Atiku Abubakar ya sake daddale batu dangane da batun tallafin man fetur, inda ya ce "Ina nan akan bakana, kuma bazan canza ba: Zan dawo da shi!"
Tun bayan da ɗan takarar shugaban ƙasar Nijeriya a jam'iyyar ADC Atiku Abubakar ya bayyana ra'ayinsa game da dawo da batun tallafin man fetur, 'yan siyasa musamman masu mulki suka kasa zaune suka kasa tsaye.
Yau ma Talata, a lokacin da Atiku ya karɓi baƙuncin jam'iyyar ADC a Abuja ya sake nanata ƙudurinsa, inda ya nuna cewa. Ƙasa mai albarkatu irin Nijeriya bai kamata ta bar al’ummarta cikin wahala ba. Nijeriya ƙasa ce mai wadatar da za ta iya kula da ‘yan ƙasarta."
Ya ƙara da cewa, a ganina, ba a auna arziƙin ƙasa da yawan kuɗin da gwamnati ke karɓa, ana auna shi ne da irin ƙarfin saye da kuma kuɗin da ke a hannun talakawa.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa, Ina son albashi ya sake samun daraja. Ina son manoma su samu damar kai amfanin gonarsu kasuwa ba tare da tsadar sufuri ta cinye ribarsu ba. Ina son iyalai su iya cika kwandonsu da kayan abinci ba tare da sun kashe duk kuɗin da ke aljihunsu ba. Ina son ‘yan kasuwa su samu damar samar da kayayyaki, ɗaukar ma’aikata da bunƙasa sana’o’insu. Shi ya sa zan dawo da tallafin man fetur da aka tsara domin taimakon al’umma.
Atiku ya ci gaba da cewa. Idan farashin man fetur ya tashi, farashin sufuri ma yana tashi. Idan sufuri ya yi tsada, farashin abinci yana ƙaruwa. Idan abinci ya yi tsada, iyalai su ne ke shan wahala. Don haka, zan kawo ƙarshen wannan mummunan yanayi da ya addabi rayuwar ‘yan Nijeriya kusan shekaru huɗu na mulkin Tinubu.
Zan tallafa wajen samar da kayayyaki a Nijeriya, rage kuɗin makamashi. Ba zan dawo da tsarin shigo da man fetur da ake samun damammakin cin hanci da rashawa ta cikinsa ba; abin da zan dawo da shi shi ne sauƙi da rangwame ga jama’a. Na sake jaddada wannan matsaya tawa ne a ranar Talata, lokacin da na karɓi shugabannin jam’iyyar ADC na Jihar Osun a Abuja.
Daga ƙarshe Atiku ya rufe da wasu alƙawura inda ya ce, "Zan tabbatar da Naira ta dawo da darajar ta, rayuwar yau da kullum ta zama mai sauƙi, sannan a samar da tsaro da kwanciyar hankali ga al’ummar ƙasa. Tsaron tattalin arziƙi. Tsaron rayuka da dukiyoyi. Da kuma ingantacciyar rayuwa ga kowane ɗan Nijeriya. Wannan ita ce Nijeriya da nake da burin ginawa tare da ku."