Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da takwarorinsa na jihohin Yobe, Sokoto da Jigawa, sun yaba wa shugaban majalisar malaman JIBWIS ta ƙasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, kan ƙoƙarinsa na inganta haɗin kan Musulmi da zaman lafiya a Najeriya.
Gwamnonin sun bayyana hakan ne a wani taron ƙasa na kwana ɗaya da JIBWIS ta shirya a Jos, jihar Plateau, kan ƙara sa hannun al’umma a harkokin siyasa da tallafawa adalci a matsayin hanyar samun haɗin kai da ci gaban Najeriya.
A yayin taron, JIBWIS ta buƙaci mambobinta a faɗin ƙasar su mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima baya tare da zaɓensu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Shugaban JIBWIS na Ƙasa mai kula da harkokin gudanarwa, Sheikh Abdulnasir Abdulmuhuyi, ya bayyana gamsuwa da ayyukan gwamnatin Tinubu-Shettima, yana cewa ta nuna ƙwazo da jajircewa wajen ci gaban ƙasa cikin shekaru uku na farko.
Shi ma Sheikh Jingir ya yi kira ga mambobin JIBWIS da su sabunta goyon bayansu ga Tinubu da Shettima domin zaɓen 2027.
Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, wanda ya yi magana a madadin gwamnonin Kano, Sokoto, Jigawa da Yobe, ya yabawa Sheikh Jingir kan jajircewarsa wajen inganta haɗin kan ƙasa da zaman lafiya tsakanin ’yan Najeriya.
A nasa saƙon fatan alheri, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya ce Najeriya ba za ta iya yin watsi da gwamnatin Tinubu-Shettima a 2027 ba, yana mai kuma yabawa Sheikh Jingir kan ƙoƙarinsa na samar da zaman lafiya da haɗin kai.
A wani ɓangare na taron, Hon. Ibrahim Kabir Masari da Gwamna Mai Mala Buni sun bayar da gudunmawar naira miliyan 300 kowannensu domin kafa Jami’ar Fortune University da Sheikh Sani Yahaya Jingir ya assasa.
Taron ya samu halartar manyan malaman addinin Musulunci, ’yan siyasa, jami’an gwamnati da mambobin JIBWIS daga sassa daban-daban na ƙasar, inda suka tattauna kan harkokin siyasa, adalci, haɗin kan ƙasa da ci gaba mai ɗorewa.
