Yayin da rikici ke ƙara tsananta tsakanin Iran da manyan abokan hamayyarta, United States da Israel, ana mai da hankali kan irin makaman da Tehran ta mallaka. Iran ta shafe shekaru tana bunƙasa ƙarfin sojinta, musamman a ɓangaren makamai masu linzami, jirage marasa matuƙa da tsarin kariyar sararin samaniya.
Iran na da ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen makamai masu linzami a Gabas ta Tsakiya. Makamai masu linzamin nata na matsakaicin zango na iya kai hari ga wurare da dama a yankin, ciki har da Isra’ila da sansanonin sojin Amurka. Wadannan makamai su ne ginshikin karfin harin nesa da Iran ke dogaro da shi.
Baya ga makamai masu linzami, Iran ta zuba jari sosai a kan jirage marasa matuki (drones), ciki har da wadanda ake kira “kamikaze” masu kai hari daya tilo. Ana kallon wadannan jirage a matsayin makamai masu saukin kera amma masu iya haifar da babbar illa, musamman idan an harba su da yawa lokaci guda.
Haka kuma Iran ta samar da tsarin kariyar sararin samaniya domin kare kanta daga hare-haren sama. Wadannan tsare-tsare na kokarin kakkabe jiragen yaki, drones da makamai masu linzami da ke shigowa, duk da cewa masana na muhawara kan yadda za su iya tinkarar manyan fasahohin yammacin duniya.
Bugu da kari, Iran na dogaro da kawaye da kungiyoyin makamai a wasu kasashe na yankin domin fadada tasirinta. Hadin wannan karfi na makamai masu linzami, drones, kariyar sama da kawance na yankin shi ne tubalin dabarun Iran yayin da take fuskantar Amurka da Isra’ila.