Amurka ta Jajanta wa Najeriya kan Harin Kwara

Ofishin jakadanci Amurka a Najeriya ya fitar da wata sanarwa a yau Juma'a inda ya yi Alla-wadai da "mummunan harin da aka kai a jihar Kwara" da ke arewacin Najeriya, inda aka kashe mutanen da har yanzu ba a kammala tantance yawansu ba.

Sanarwar da ofishin ya fitar a shafukan sada zumunta ta ce "muna miƙa alhininmu ga iyalan waɗanda wannan kisa na rashin hankali ya shafa, kuma muna maraba da matakin shugaba Tinubu na tura dakaru domin tsare ƙauyukan da ke yankin".

A ranar Talatar makon nan ne wasu mahara da ake zargin masu tsattsauran ra'ayin addini ne suka kai hari kan ƙauyukan Woro da kuma Nuku a ƙaramar hukumar Kaiama da ke jihar Kwara, inda suka kashe mutanen da ake hasashen sun zarta 100.

Ɗan majalisar jihar Kwara mai wakiltar yankin, Sa'idu Baba Ahmed ya shaida wa BBC cewa an yi jana'izar mutum 78 a yammacin ranar Laraba.

Shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya ɗora alhakin harin kan ƙungiyar Boko Haram wadda ta shafe sama da shekara 15 tana kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

A baya-bayan shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin cewa ana yi wa mabiya addinin Kirista a Najeriya kisan gilla, lamarin da gwamnatin ƙasar ta musanta.

Gwamnan jihar Kwara ya ce a harin na ranar Talata an kashe "Musulmai 75" yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ƙididdige yawan mutanen da aka kashe.

Haka nan gwamnan ya ce an kashe mutanen ne saboda sun ƙi bin wani baƙon koyarwar Musulunci da maharan suka so su ƙaƙaba musu.

Post a Comment

Previous Post Next Post