Ƴansanda a jihar Maharashtra na Indiya sun ce sun tsare wasu ƴan Najeriya 109, waɗanda suka kama kan laifin zama ba bisa ka'ida ba a ƙasar, inda suka ce sun ƙwace hodar iblis mai nauyin kilogram biyu a wajen miutanen.
Hukumomin ƙasar sun ce babu wanda yake da cikakkun takardun zama cikin mutanen, waɗanda ke zaune a birnin Nalasopara da ke gabashin ƙasar.An kai samame yankin ne da misalin karfe 6 na safe, a cewar mataimakiyar kwamishinan ƴansandan yankin Poornima Chowgule-Shringi.
"A lokacin samamen ne muka samu damar ƙwace hodar iblis mai nauyin giram 2 daga hannun wani mutum," in ji ta.
An sha samun hannun ƴan ƙasashen waje daga Najeriya, Uganda da kuma Ghana waɗanda ke rayuwa a Nalasopara da Achole da kuma Tulinj a batun safarar miyagun ƙwayoyi, in ji jami'ar ƴansandan.