Ƙungiyar siyasa ta Kwankwasiyya ta musanta rahotanni da ke iƙirarin cewa an fita da jagoran jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso waje don neman lafiya.
Mai magana da yawun ƙungiyar Kwankwasiyya a Najeriya, Captain Mansur Kurugu, ya shaida wa BBC cewa Kwankwaso ya tafi ƙasar waje ne don wata buƙatarsa."Abin da zai ƙara tabbatar da haka shi ne ranar Laraba kafin balaguronsa ya shiga jihar Kano kuma ya gana da mutane daban-daban. A safiyar yau Alhamis kuma dubban mutane daga karamar hukumar Dawakin Kudu sun kawo masa ziyara aka tattauna sannan ya zarce zuwa kasuwar Singer don jajantawa ƴan kasuwar da suka rasa duƙiyoyi," in ji Mansur.
Ya ce mutumin da ba shi da lafiya ba zai yi irin waɗannan al'amura ba, inda ya ce waɗanda ba su ji daɗin tarbar da aka yi masa ba a Singer su suka kirkiro da labarin.
"Babu wata magana ta rashin lafiya ko wata damuwa. Kawai masu jin tsoro ne ke son kawo labarin don disashe irin karɓuwar da Kwankwaso yake ƙara samu," in ji shi.
Ya ce jagoran Kwankwasiyyar zai koma Najeriya nan ba da daɗewa ba idan ya kammala abin da ya je yi a ƙasar waje.
Balaguron da Sanata Kwankwaso ya yi zuwa waje dai ta karaɗe shafukan sada zumunta inda ake ta yaɗa cewa ya fita ne don neman lafiya.