Wasu ƴanbindiga sun hallaka mutum biyar tare da yin garkuwa da wasu da dama bayan harin da ƙwantan ɓauna da suka kai wata kasuwa a jihar Zamfara.
Mazauna yankin na komawa gida daga kasuwar Maga a karamar hukumar Bukkuyyum da yammacin ranar Laraba lokacin da aka kai musu harin.Lamarin ya saka fargaba a zuƙatan al'ummomi da ke kusa.
"Aƙalla mutum biyar aka tabbatar da mutuwarsu, sannan ba a ga wasu da dama ba zuwa yanzu. Ana ci gaba da aikin ceto, sai dai fargaba na ƙara yaɗuwa a tsakanin al'ummomi," kamar yadda wata majiyar tsaro ta bayyana.
Mazauna yankin dai na buƙatar gwamnati ta kai musu ɗaukin gaggawa domin nemo waɗanda suka ɓata da kuma dakatar da hare-haren da ake kai musu.
Harin na zuwa ne kwana guda bayan artabu tsakanin sojoji da ƙungiyoyin ƴanbindiga ya janyo mutuwar dakaru da ƴan ta'adda da dama a karamar hukumar Maru na jihar ta Zamfara.