Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya ce Najeriya za ta ƙarfafa hulɗar dangantaka da Falasɗinawa da kuma kyautata ayyukan jin-ƙai a Gaza.
Tuggar ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin jakadan Falasɗinawa a Najeriya, Muhannad Halmouri a Abuja, babban birnin Najeriya.Jakadan na Falasɗinawa ya nuna jin daɗinsa kan daɗaɗɗiyar goyon baya da Najeriya ke bai wa Falasɗinu da kuma ganin ta samu cin gashin kai.
Halmouri ya bayyana irin yanayin jin-ƙai da Gaza ke fama da shi, ciki har da matsalolin tsaro da ake fuskanta da kuma taƙaita shigar da agaji yankin.
Jakadan Falasɗinawan ya ce gwamnatin Falasɗinawa na cike da farin ciki kan tattaunawar da aka yi a Najeriya don ganin dangantakar ɓangarorin ta ɗore.
Tuggar ya tabbatar da cewa Najeriya za ta yi abin da ya kamata wajen ganin an shawo matsalolin da Falasɗinawan ke fuskanta ta hanyar tattunawar diflomasiyya.
Najeriya dai ta daɗe tana nuna goyon baya ga Falasɗinawa a rikicinsu da Isra'ila, inda a watan Nuwambar 2024, shugaba Tinubu ya yi kira ga shugabannin duniya da su taimaka wajen kawo karshen farmakin soji da Isra'ila ke yi a Gaza da kuma ƙara nanata goyon baya na samar da mafita ta ƙasashe biyu.