Masar Ta Kaddamar Da Babban Gidan Tarihi Na Al’adun Da

 Gwamnatin Masar ta ƙaddamar da sabon Babban Gidan Tarihi na Masar (Grand Egyptian Museum), wanda aka gina domin nuna girman tsofaffin al’adunta da kuma adana muhimman kayan tarihin da suka shafi daular Fir’auna.

Grand Egyptian Museum

Wannan gagarumin gini da ke kusa da harabar Pyramid na Giza ya kasance ɗaya daga cikin manyan gidajen tarihi mafi girma a duniya, inda aka ajiye ɗaruruwan abubuwan tarihi da suka haɗa da gumaka, kayan sarauta, da kayan ado na tsoffin sarakunan Masar.

A cewar Ministan Al’adu na Masar, Ahmed Issa, wannan gida tarihi yana nufin bai wa duniya damar ganin tarihin Masar kai tsaye ta hanyar fasaha da ilimi. “Wannan ba kawai gidan tarihi ba ne, alamar alfahari ce ta al’adun Masar da gudunmawar da ta bayar wajen gina wayewar dan Adam,” in ji shi.

An fara aikin ginin gidan tun shekarar 2010, amma ya jinkirta saboda wasu matsalolin tattalin arziki da annobar COVID-19. Yanzu dai an bayyana shi a hukumance a matsayin mafi girma gidan tarihi guda ɗaya a duniya da aka keɓe don al’adun ƙasa ɗaya.

Masar ta ce tana sa ran sabuwar cibiyar za ta ja hankalin miliyoyin masu yawon bude ido daga sassan duniya, wanda hakan zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.


Post a Comment

Previous Post Next Post