Tauraron matashin ɗan wasan Barcelona, Lamine Yamal, ya tabbatar da cewa ya rabu da budurwarsa, Nicole, amma ya bayyana cewa ba saboda cin amana aka rabu ba.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Yamal ya ce: “Ba mu tare yanzu. Ba saboda wani cin amana ba ne. Mun yanke shawarar rabuwa ne kawai, kuma hakan shi ne gaskiya. Duk abin da ake yaɗawa yanzu bai da alaƙa da mu. Ban yi wa kowa cin amana ba, kuma ban kasance da wani ba.”
Sanarwar tasa ta biyo bayan jita-jitar da ke yaduwa a kafafen sada zumunta game da dalilin rabuwarsu, inda Yamal ya roƙi masoyansa da su guji yada ƙarya tare da girmama sirrinsa.