A wannan shekara ta 2025, abin da ya fi ɗaukar hankali a Capitol Hill ba doka ce ta gina cimma dai-daituwa tsakanin jam’iyyu ba, ba kuma takunkumin TikTok ba ne, a’a, shi ne “Labarin Kisan Kiyashi na Najeriya” da aka shirya saboda damfara.
Hanyar damfarar na da sauƙi: ka yi ihu ka ce “ana kashe Kiristoci!”, ka nuna bidiyon bandits da ke hawa babura, sannan ka jira dalolin Amurka su zubo kamar ruwan sama daga kasafin Pentagon.
Donald Trump, wanda a ranar 31 ga Oktoba ya sake sanya Najeriya cikin jerin “Ƙasashen da ke da Matsala ta Musamman” (CPC) bisa zargin cewa ana “yankan Kiristoci” da sunan “’yan jihadi.”
Wandanda su ka kulla wannan ba a Fadar White House su ke ba. Su na zaune ne a gidan haya a unguwar Georgetown.
’Yan Damfara a Washington daga Najeriya — tsofaffin ma’aikatan bankuna, tsoffin manazarta, da masu kiran kansu “masu fafutuka” waɗanda suka gano cewa babu abin da ke buɗe aljihun Amurkawa da sauri kamar labarin kisan kiyashi.
Ba su taba ganin coci yana ƙonewa da idonsu ba.
Ba su taba zuwa kauyen da aka kai hari ba.
Suna da PowerPoint, donor dinner, da lambar waya ta sanata wanda yake rubuta “Niggeria” da harafi biyu na g.
Mataki na Farko: Lokacin Biden
A 2020, lokacin da Trump ya fara sanya Najeriya cikin CPC, abin ya ɗan yi zafi na ɗan lokaci. Sai aka dakatar da tallafi. Labarai suka cika kafafen yada labarai.
Sai Biden ya hau mulki, ya karanta rahoton Ma’aikatar Harkokin Waje, ya ga gaskiya, kuma ya cire Najeriya. Me ya gani?
Saboda hukumar USCIRF ta kasa gano wannan “kisan kiyashi”.
Shin akwai tashin hankali a Arewacin Najeriya? Akwai, kuma ya ragu.
Shin ana kisan kare dangi ga Kiristoci? Babu a cikin bayanai.
’Yan fashi suna kashe manoma, manoma suna ramawa.
Musulmai suna mutuwa, Kiristoci suna mutuwa, masu bin gargajiya suna mutuwa.
Tsarin da ya fi fitowa fili shi ne talauci, ba addini ba.
Sai ’yan damfara suka firgita.
Kungiyoyinsu “na jin ƙai” da aka yi rijista a jihar Delaware, amma ake tafiyar da su daga WhatsApp, suka rasa kuɗin da suke tsotsa.
Wani ma sai da ya sayar da Range Rover ɗinsa.
Wata kuma dole ne ta hau economy class zuwa Abuja.
Trump 2.0: Sake Dawowa da Tsohuwar Damfara
Yanzu shekara ta 2025 ce. Trump ya dawo, Truth Social na ci, kuma kwatsam “kisan kiyashi” ya sake zama “batun addini.”
Bidiyoyin da suka fito tun 2018 sun dawo, yanzu da sautuka masu ban tsoro.
.A bayan fage, damfarar na tafiya a kan tsari:
Mataki na 1: A fitar da “rahoton bincike” ga wani think tank mai ra’ayi ɗaya. A ambaci “dubban da aka kashe” ba tare da an ba da kwanan wata ba, wurin da aka kashe su, ko sunaye ba.
Mataki na 2: A shirya “balaguron bincike.” Otel mai tauraro biyar. Per diem. Selfie da “wadanda suka tsira” — waɗanda a gaskiya su ne ma’aikatan otel din.
Mataki 3: Hada kai da “Religious Freedom Industrial Complex.”
’Yan Evangelical su ba da gudummawa. Majalisa ta ware kuɗi.
Kudin ya zubo zuwa “shirin tsaro,” “yaɗa wayar kai,” da “kuɗin gudanarwa” — ma’ana, gidaje a Dubai.
Lissafi Bai Yi Karya Ba (Amma Masu Damfara Suna Yi)
• Yawan al’ummar Najeriya: ~50% Musulmi, ~50% Kiristoci.
• Yawan mutuwa sakamakon tashin hankali a shekara: 8,000–10,000 (rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya).
• Bangaren addini na waɗanda ke mutuwa: kusan daidai da yawan jama’a.
• Kuɗin CPC (2020–2021): $47 miliyan a matsayin “tallafin ’yancin addini.”
• Adadin da ya isa wurin waɗanda abin ya shafa: [an boye saboda dariya].
Gwamnatin Najeriya mai cike da kura, amma ba sakarya ba ce. Ta mayar da martani:
“Wannan ba laifin addini ba ne, laifin fashi da makami ne,” in ji Ma’aikatar Harkokin Waje.
“Mun kashe ’yan ta’adda 3,000 a bana. Rabinsu Musulmai ne. Ina CPC ɗinsu?”
GASKIYAR ABUN TSORO
Mu faɗi gaskiya: Najeriya na da matsaloli. Boko Haram mugaye ne. Rikicin makiyaya da manoma na hallaka kowa. Cin hanci na karuwa.
Amma juyar da wannan bala’in ƙasa zuwa dabarar neman kuɗi ta addini ba ya taimakawa kowa — sai dai ’yan tsakiya masu fasfo ɗin Amurka da harshen Najeriya.
Irin wannan damfara ce da ke lalata gaskiya, tana mayar da mutuwar mutane zuwa PowerPoint presentation. Addininsu ba Kiristanci ba ne, ba Musulunci ba ne, kasuwanci ne.
Kuma ibadarsu mafi tsarki shine — budget.
YADDA ZA A LALATA WANNAN DAMFARAR
1. A Nemi hujja, ba zance ba. A daina dogaro da bidiyoyi ko labaran WhatsApp. A nemi bayanan Majalisar Ɗinkin Duniya ko Tarayyar Afirka.
2. A bi sawun kuɗi. Duk wata NGO da ke karɓar kuɗin CPC ta bayyana kasafinta — har da kwalban ruwan da suka sha.
3. A Tura ’yan majalisa su ga gaskiya. Ba tare da ’yan tsaro ko "per diem" ba. Bari su ga ramin rijiyar da bai taɓa kammalawa ba saboda kuɗin ya tafi hannun “consultant” a Virginia.
A kira shi da sunansa na gaskiya. Ba kisan kiyashi ba ne —cinikin ƙarya ne da aka lullube da suturar addini da kuma neman kudin haram.
