An Tuna Baya Kan Rikicin Tinubu Da Jonathan Kan Kisan Kiristoci a Najeriya

 An sake jawo hankalin jama’a kan yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taɓa caccakar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a baya, sakamakon yadda ake kashe Kiristoci a Najeriya a lokacin mulkinsa.

A wancan lokacin, Tinubu ya yi kakkausar suka ga gwamnatin Jonathan, yana mai cewa rashin tsaro da kisan mutane musamman Kiristoci a Arewa maso Gabas na nuna gazawar gwamnati wajen kare rayukan ‘yan ƙasa.

Wasu masu sharhi sun sake tuna wannan lamari a yanzu, musamman bayan da Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargi da tauye ‘yancin gudanar da addini da kuma kisan Kiristoci.

Masu lura da al’amura sun ce, wannan tuna bayan na nuni da yadda siyasa ke sauya fuska, inda waɗanda ke suka a da sukan fuskanci irin ƙalubalen da suka zargi wasu da su a baya.

Post a Comment

Previous Post Next Post