Majalisar ƙoli kan harkokin shari'ar musulunci a Najeriya (SCSN) ta sake nanata kiranta da a tsige shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar (INEC), Joash Amupitan, domin a cewarta, ba zai iya yin adalci a babban zaɓen ƙasar mai zuwa ba.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar, wadda sakatare-janar ɗinta, Nafi’u Baba Ahmad ya sanya wa hannu, inda ta ce kiran bai da alaƙa da addininsa ko ƙabilanci.Ta ce wannan takardar da ta fitar, ƙarin bayani ne kan wadda ta fitar a baya a ranar 28 ga watan Janairu, wadda a cewar majalisar aka canja wa fassara. "Wannan ne ya sa muka saka zama domin fitar da sabuwar takarda domin fayyace matsayarmu."
"Babu ruwanmu da batun addini, magana ake yi ta nagarta da inganci. Najeriya ta gudanar da zaɓuka da dama tun daga samun ƴancin kai a 1960 zuwa yanzu, kuma ba a taɓa samun lokacin da aka yi amfani da addini wajen amincewa ko ƙin amincewa da sakamakon zaɓe ba."
Majalisar ta ce daga shugaban hukumar zaɓen Najeriya na 1960, Eyo Esua zuwa yanzu, hukumar ta yi shugabanni guda 13, "amma a ciki Farfesa Attahiru Jega da Farfesa Mahmood Yakubu ne kawai musulmai, kuma duk da haka ba a taɓa samun lokacin da musulman Najeriya suka ƙi amincewa da zaɓe saboda bambancin addini ba."
Sanarwar ta ƙara da cewa buƙatar cire shugaban na yanzu, Farfesa Amupitan ba magana ake yi ta addininsa, "magana ake yi ta abubuwan da ya aikata a baya, musamman takardar da ya jagoranci rubutawa a 2020, wadda a ciki ya yi amfani da kalamai masu zafi da cin zarafi da cin mutunci musulman Najeriya da yankin arewa da Usman Ɗanfodio."
Majalisar ta ce a cikin takardar koken ya yi zargin ana yi wa kiristocin Najeriya "kisan kiyashi", "sannan ya yi yunƙurin alaƙanta matsalar tsaro da ake fuskanta a arewacin Najeriya da jihadin Ɗanfodio na ƙarni na 19, wanda ba daidai ba ne, kuma yunƙuri na tayar da zaune tsaye. Sannan abin ban haushi suka miƙa wannan ƙanzon kuregen zuwa ƙasashen waje domin nuna Najeriya a matsayin ƙasar da kiristoci ba su da ƴancin addini."
Majalisar ta ƙara da cewa tun bayan fitar da takardar da ake magana, har yanzu shugaban na INEC bai fito ya nesanta kansa ba, sannan ta ƙara da cewa shugabantar hukuma irin ta zaɓe na buƙatar mutum wanda ba ya nuna bambancin addini da ƙabilanci.