Hukumomin Turkey sun ce tsarin kariyar sama na NATO ya lalata wani makami mai linzami da aka harba daga Iran yayin da yake shawagi a saman yankin Bahar Rum.
Ma’aikatar tsaron Turkiyya ta bayyana cewa an kakkabe makamin cikin gaggawa kafin ya shiga sararin samaniyar kasar. An ce sassan makamin sun fadi a yankin Hatay da ke kudancin Turkiyya, amma ba a samu rahoton asarar rai ko jikkata ba.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ke kara tsananta a yankin tsakanin Iran da kawayen Yamma. Wannan shi ne karo na farko da aka ce wani makami daga Iran ya yi barazanar shiga sararin samaniyar kasar da ke mamba a NATO tun bayan barkewar rikicin.
Jami’an NATO sun sake jaddada goyon bayansu ga Turkiyya, suna mai cewa kawancen na da cikakken shiri domin kare kasashe mambobinsa daga duk wata barazana ta sama.