Majalisar ƙoli kan harkokin Shari'ar musulunci a Najeriya (SCSN) ta sake sabunta kiran da ta yi na a tsige Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasar (INEC), Joash Amupitan, gabanin babban zaɓen 2027, inda ta bayyana shi a matsayin barazana ga amincin tsarin dimokraɗiyyar Najeriya.
A wata hira da ya yi da BBC, shugaban majalisar, Sheikh Bashir Aliyu Umar, ya bayyana matsayarta kan shugban hukumar inda ya yi gargadin cewa Musulmin Najeriya ba za su amince ko halasta duk wani sakamakon zaɓe da aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Amupitan ba.Sheikh Umar ya ce matsayar majalisar ta samo asali ne a kan abin da ta bayyana a matsayin abubuwan da shugaban hukumar ta INEC ya aikata a baya, musamman ma wani takaitaccen bayani na shari'a da ake zargin ya rubuta wanda ke nuna cewa ya amince da batun cewa ana yi wa Kirista kisan kiyashi a Najeriya – ikirarin da gwamnatin tarayya ta sha yin watsi da shi.
''Har yanzu muna kan bakarmu, saboda shi shugaban hukumar zaɓe bai fito ya musanta cewa wannan abun ba haka ba ne. Ya na nan kan iƙirarinsa, bai ma ga cewa wannan wani abu ne da zai fito ya yi magana a kai ba,'' in ji shi Sheikh Umar.
A cewarsa, matsayin da shugaban hukumar ta INEC ya ɗauka tamkar farfaganda ne mai raba kan jama'a tare da sanya shakku sosai kan ko zai iya adalci a matsayinsa na shugaban hukumar zaɓen Najeriya.
Shugaban majalisar ƙolin kan harkokin Shari'ar Musulunci a Najeriya ya ce: "Mu muna ganin duk wanda yake da irin wannan matsayi, ya kamata gwamnati ta sake nazari, saboda matsayi ne wanda yake da matuƙar muhimmanci, ana son a samu wanda babu ruwansa da ɓangaranci, mai adalci kuma wanda ke nuna ba sani ba sabo a kan abin da zai yi.''
Sheikh Bashir Umar ya ƙara da cewa "Abin da ya dace shi ne ya yi murabus, idan kuma bai yi ba ya kamata gwamnati ta yi masa murabus saboda duk abin da za a yi na zaɓen nan, wannan zai sanya rashin aminci a cikin zukatan mutane.''