Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi watsi da zargin da Amurka ta yi mata, na cewa ana tauye ‘yancin gudanar da addini da kuma yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a cikin ƙasar.
A wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin ta bayyana cewa Najeriya ƙasa ce mai mutunta ‘yancin addini, inda Musulmai da Kiristoci da masu bin sauran addinai ke gudanar da ibadunsu cikin walwala da zaman lafiya.
Gwamnatin ta ce rahoton da Amurka ta fitar ba ya nuna hakikanin halin da ake ciki a ƙasar, domin ana samun matsalolin tsaro da ke shafar kowa ba tare da la’akari da addini ba.
Ta kuma jaddada cewa ana ci gaba da ɗaukar matakai don tabbatar da zaman lafiya da adalci a duk sassan ƙasar, tare da kira ga ƙasashen duniya da su guji yanke hukunci bisa bayanan da ba su da inganci.