Rundunar sojin ƙasan Najeriya ta tabbatar da harin ƙunar bakin-wake da aka kai masallacin Maiduguri, inda ta ce ɗan Boko Haram ne ya kai harin.
yammacin jiya Laraba ne ɗan ƙunar bakin-waken ya kai hari a wani masallaci da ke kasuwar Gamborou a cikin garin Maiduguri a daidai lokacin da musulmi suke gudanar da sallar Maghriba.A wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce, "binciken farko-farko ya tabbatar da cewa ɗan Boko Haram ne ya kai harin na ƙunar bakin-wake, inda ya kashe kansa da mutum biyu a nan take."
Sanarwar ta ƙara da cewa wasu mutum biyu daga cikin aƙalla 32 da suka jikkata sun rasu a asibiti, sannan akwai wasu guda biyu da ke cikin matsanancin hali.
A ƙarshe, rundunar ta yi kira ga al'ummar Maiduguri da su kwantar da hankalinu, "sannan su zama masu sa ido tare da nesantar tarukan mutane, sannan su kai ƙarar duk wani abu da ba su gane ba ga jami'an tsaro cikin gaggawa."