Da Taron Raɗin Suna Da Na Ɗaurin Aure Duk Al'adu Ne

ƘARAMIN SANI ƘUƘUMI NE

Shahararren malamin addinin Musuluncin nan kuma ɗaya daga cikin kwamishinonin jihar Sokoto, Dr Jabir Sani Maihulla ya bayyana cewa:

"Taron zanen suna kamar taron ɗaurin aure ne. Annabi S.A.W bai tãra kowa wajan ɗaurin aure ba, Annabi bai tãra kowa wajan zanen suna ba. Taron ɗaurin aure da taron zanen suna duk ɗaya ne. Babu wanda As-Sunnah, babu wanda ab-Bid’ah, kowanne al’ada ne. Idan ka ga dama ka raba goro ka gayyaci mutane a zo a ɗaura ma aure, in ka ga dama ba ka gayyatar kowa, daga kai sai babanta sai shedu biyu (akan inganta hadissan shedu). Wajen walima ake tara jama'a."

Amma abin mamaki babu wanda ya taɓa tayar da ƙayar baya kan batun taruwa a wurin bukin ɗaurin aure, sai dai batun taruwa wurin raɗin suna, bayan ga shi malam ya bayyana cewa dukkansu babu guda da yake addini a cikinsu, dukkansu al'adu ne, kuma kowace al'umma da yadda take gudanar da tata al'adar.

A ganinku mene ne ya kawo waɗannan batutuwan da suka shahara ana jifar juna da su?

Post a Comment

Previous Post Next Post