Gwamnatin Saudi Arabia ta buƙaci ƙungiyoyin ’yan aware na Yemen da su gaggauta ficewa daga jihohin da suka ƙwace, tana mai cewa ci gaba da riƙe waɗannan yankuna na barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin.
A cikin wata sanarwa, Saudiyya ta bayyana damuwa kan yadda ’yan aware ke ci gaba da mamaye wasu muhimman jihohi, duk da yarjejeniyoyin siyasa da aka cimma a baya domin daƙile rikicin Yemen. Riyadh ta ce irin wannan mataki na iya lalata ƙoƙarin da ake yi na dawo da zaman lafiya da haɗin kan ƙasar.
Sanarwar ta kuma jaddada goyon bayan Saudiyya ga halastacciyar gwamnatin Yemen, tare da kiran dukkan bangarorin da su mutunta yarjejeniyoyin da aka sanya wa hannu, su kuma fifita tattaunawa maimakon amfani da ƙarfi.
Masu lura da al’amuran siyasa na ganin wannan buƙata na Saudiyya na iya ƙara tsananta takaddama tsakanin bangarorin da ke rikici a Yemen, musamman a yankunan kudanci, inda rikicin iko ke ci gaba da hana samun dawwamammen zaman lafiya.