A duk lokacin da aka yi batun juyin mulki a nahiyar Afirka, mutumin da ke fara faɗowa a ran jama'a shi ne Janar Gamal Abdel Nasser, soja ɗan ƙasar Misra da ya fara hamɓare wata gwamnati a nahiyar Afirka a 1952.
Kuma tun daga lokacin ne nahiyar Afirka ke fuskantar juyin mulki, inda zuwa yanzu an yi juyin mulki fiye da 220, ciki har da fiye 109 da aka samu nasara, sannan aka samu nasarar daƙile fiye da 111.Ƙididdiga ta nuna cewa daga cikin ƙasashen nahiyar Afirka 54, 45 daga ciki sun fuskanci juyin mulki ko da sau ɗaya ne.
Alƙaluma daga Powell and Thyne sun nuna cewa ƙasar Sudan ce ta fi kowace ƙasa yawan juyin mulki – inda take da 16 ko dai waɗanda aka samu nasara ko kuma waɗanda aka gaza samun nasarar aiwatarwa.