Majalisar Hadakar Kungiyoyin Musulunci A Zamfara Sun Yi Allah-Wadai Da Kudurin Trump Na Soke Shari'a Musulunci

Kungiyar Haɗakar ƙungiyoyin Musulunci ta jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Dr. Aliyu Muhammad Jangebe,  ta gudanar da taron a Gusau babban birnin jihar Zamfara shugaban ya jaddada cewa ba za su lamunci ƙudurin Trump na soke shari'ar musulunci ba kamar abin da ya shafi: soke hukuncin kisa da hukumar Hisabah da sauransu.
Shugaban ya jaddada cewa babu wani Kirista da ake tilasta mashi da shari'a a kotunan musulunci. Hasali ma tana kare haƙƙoƙan wanda ba musulmi ba.

Kawo yanzu jihohin arwacin guda 12 ne suke aiwatar da shari'ar. Amma  jihar Zamfara ita ce wadda ta fara ƙaddamar da shari'a dukkan fadin ƙasar, a lokacin tsohon gwamnan jihar Zamfara Alhaji Sani Yariman Bakura a shekarar 1999.

Post a Comment

Previous Post Next Post