Wani tsohon soja kuma masanin tsaro wato Manjo Janar Yahaya Shinko mai ritaya ya zargi shugaba Bola Ahmed Tinubu da yin shiga sharo ba shanu, wajen kai wa Jamhoriyar Benin doki wajen daƙile juyin mulki.
Ya ce hakan ya kamata ya faru ne tare da Sani da kuma sahalewa ta ta 'yan majalusun kasa. Amma ya yi gaban kansa wajen tura dakarun sojin Najeriya Zuwa Kasar ta Benin.
Ya ƙara da cewa: Najeriya ta wannan ne daidai lokacin da ake kumfar bakin cewa ƙasar Amurka ta yi barazanar shigowa ƙasar ba tare da izinin Najeriyar ba.
Ya tabbatar da cewa ana iya hakan amma sai an samu yardar majalisun dattijai da wakilai. Kuma da yardar ita ƙasar ko ita c ta nemi ɗokin. Ya kuma ce ana fama da matsalar tsaro a cikin gida amma ba a yi amfani da jiragen da aka aika Benin ba wajen yaƙar ƴanta'adda da ke tada zaune tsaye a cikin ƙasa.
.jpeg)