Gwamnatin ƙasar Benin ta bayyana cewa rundunar sojin ƙasar ta hargitse wani yunƙurin juyin mulki da aka yi ƙoƙarin ƙaddamarwa, bayan wasu sojoji sun bayyana a gidan talabijin na ƙasa suna mai da’awar cewa sun kifar da Shugaba Patrice Talon.
Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun mamaye gidan talbijin ne da safiyar Talata, inda suka yi jawabi cewa sun karɓi mulki domin “kare dimokuraɗiyya da adalci”. Sai dai mintuna kaɗan bayan haka, an katse taron nasu lokacin da sojojin da ke goyon bayan gwamnati suka kutsa suka kuma ƙwace ikon gidan talbijin.
Mai magana da yawun gwamnati, Wilfried Houngbédji, ya tabbatar da cewa zaman lafiya ya koma cikin birnin Cotonou, tare da jaddada cewa Shugaba Talon yana nan kan karagar mulki. Ya bayyana lamarin a matsayin “yunkuri marar nasara da wasu ‘yan kaɗan daga cikin jami’an soja suka shirya”, yana mai yabawa sojojin da suka kare martabar ƙasar cikin gaggawa.
Yunkurin juyin mulkin ya faru ne a wani lokaci da yankin Yammacin Afirka ke fama da hare–haren juyin mulki, inda kasashe irin su Nijar, Mali da Burkina Faso suka fuskanci tangardar siyasa a ‘yan shekarun nan. Masana na cewa waɗannan al’amura na nuna irin ƙalubalen da siyasa ke fuskanta a yankin.
Hukumomin Benin sun ce sun fara bincike a kan waɗanda ke da alaka da yunkurin, tare da alƙawarin hukunta duk wanda aka samu da hannu a cikin wannan shiri.