Muhawara ta ɓarke a fagen siyasar Najeriya, bayan wata ganawa da tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar, ya yi da tsohon shugaban ƙasar Good Luck Ebele Jonathan.
'Yan siyasar biyu dai basu fito fili sun yi bayanin abubuwan da suka tattauna ba, amma mutane da dama na alakanta ganawar ta su da shirye shiryen tunkarar zaben shugaban ƙasar na 2027.Ana dai raɗe raɗin cewa dukkansu, na da sha'awar tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Ganawar jiga jigan 'yan siyasar ta gudana ne a Abuja inda Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Najeriyar Good Luck Jonathan har gida, duk da irin tsamar siyasar da ke akwai a tsakaninsu, duba da cewa Atikun na cikin wadanda suka jagoranci kifar da gwamnatin Jonathan a zaɓen 2015.