Shugaban Amurka Donald Trump na shirin sanya hannu kan wata sabuwar dokar zartaswa da ake kira “one-rule executive order” domin bai wa gwamnati damar aiwatar da manyan dokokin Artificial Intelligence (AI) ba tare da amincewar jihohin ƙasar ba. Wannan matakin, in ji rahotanni, zai kawar da cikas da jihohi ke yi wajen taƙaita amfani da AI a fannoni daban-daban.
A cewar jami’an da ke kusa da shirin, dokar za ta mayar da gwamnatin tarayya ita ce babbar mai yanke hukunci kan tsare-tsaren AI, maimakon barin kowace jiha ta kafa nata ƙa’idoji. Masu sukar dokar sun ce hakan zai iya rage ikon jihohi da kuma jefa al’umma cikin barazana, domin AI na buƙatar tsauraran matakan tsaro. Amma ɓangaren Trump ya ce dokar za ta hanzarta kawo ci gaba a fannin ƙere-ƙere.
Masu sharhi sun bayyana cewa Trump na ganin AI a matsayin muhimmin ginshiƙi na bunkasar tattalin arzikin Amurka a shekaru masu zuwa. Ya sha cewa dokokin jihohi suna takurawa masana’antu, suna hana Amurka yin takara da kasashen kamar China da UK wadanda ke tafiya gaba da AI. Sabuwar dokar za ta bai wa kamfanoni damar haɓaka sababbin fasahohi cikin sauri.
Sai dai masana harkar tsaro sun nuna damuwa cewa hakar Trump na iya haifar da matsala wajen kariyar bayanai da kuma kare al'umma daga amfani mara kyau na AI. Wasu sun gargadi cewa bisa ga tsarin doka, kawar da ikon jihohi ka iya haifar da rikici tsakanin gwamnati da kotuna.
Ana sa ran Trump zai sanar da dokar a hukumance nan ba da jimawa ba, kuma za a ga yadda jihohin Amurka za su karɓi wannan sabon tsarin. A cewar masana, wannan matakin na iya zama ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen AI da za su yi tasiri a duk fadin duniya.