IAEA Ta Tabbatar Da Lalacewar Wasu Gine-Gine A Cibiyar Nukiliyar Natanz Ta Iran

 Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, wato International Atomic Energy Agency (IAEA), ta tabbatar da cewa wasu gine-gine sun lalace a cibiyar nukiliyar Natanz nuclear facility da ke Iran, bayan nazarin hotunan tauraron dan adam.

Natanz nuclear facility

A cewar hukumar, lalacewar ta fi shafar gine-ginen kofar shiga cibiyar tace sinadarin uranium ta Natanz, daya daga cikin muhimman wuraren da Iran ke amfani da su wajen inganta sinadarin uranium. Sai dai hukumar ta ce babu wata alamar fitar gurbataccen radiation mai illa, kuma ba a samu wata babbar illa a bangaren da ke karkashin kasa ba.

Natanz na daga cikin wuraren da kasashen duniya ke sa ido a kai dangane da shirin nukiliyar Iran, kuma a baya ma ta taba fuskantar hare-hare da lalacewa. Tabbatarwar da IAEA ta yi na zuwa ne a daidai lokacin da rikici da tashin hankali ke kara kamari a yankin.

Hukumar ta ce za ta ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki tare da tattara karin bayanai domin tabbatar da tsaro da kiyaye dokokin nukiliya na kasa da kasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post