Tafiye-tafiye ta jirgin sama sun funkanci cikas a yawancin ƙasashen Gabas ta Tsakiya, sakamakon rikicin da ake yi a yankin.
A wani ɓangaren, jiragen Emirates daga Daular Larabawa sun fara tashi.Wasu jiragen sun tashi daga kasashen Faransa da Birtaniya da Jamus da Italiya da Switzerland, amma an soke tashin jirage da dama.
Amurka da Isra'ila dai na ci gaba da kai munanan hare-hare a Iran
Zai yi wuya a san ainahin abin da ke faruwa a Iran, sakamakon rashin sadarwar intanet.
Amma mutanen da suka samu dama sun bayyana halin da ake ciki wanda ya fi kamari a birnin Isfahan da cibiyar makamin nukiliyar Iran ke ciki.