Iran ta yi kira ga masu zanga-zanga su miƙa wuya

Ƴansanda a Iran sun yi kira ga masu zanga-zanga da suka kwatanta da 'waɗanda hukumomin ƙasashen waje suka yaudara' da su miƙa wuya.

Ahmad Reza Razan ya faɗa wa gidan talabijin na ƙasar cewa idan suka miƙa wuya cikin kwanaki uku masu zuwa, za a rage musu girman hukunci.

Hukumomi a Iran ɗin sun ci gaba da ja daga tsakaninsu da masu zanga-zangar, inda} kwatanta su da waɗanda aka yaudara domin fito wa zaga-zanga, da kuma son tumɓuke gwamnati.

Dukkan ɓangarorin mulki a ƙasar, kama daga ɓangaren zartaswa, majalisa da kuma shari'a sun yi kira da a ɗauki tsauraran matakai da kuma hukunta masu zanga-zangar.

Post a Comment

Previous Post Next Post