Shago (ko kuma Shagon Mafara). Asalin sunansa Abubakar, mahaifinsa Muhammad, shi ne fitaccen ɗan damben gargajiya da aka taɓa yi a tarihin ƙasar Hausa, wanda ya fito daga jihar Zamfara. An haife shi a garin 'Yar Kahoji. Ya fara sana'ar Dambe tun yana yaro. An fi saninsa da bajintarsa da kuma yadda mawaƙinsa, Alhaji Muhammadu Ɗan Anace, ya rera masa waƙoƙi na musamman da suka ƙara daukaka sunansa.
Shago ana kallonsa a matsayin ɗan dambe mafi hatsari da aka taɓa yi. A cewar mawaƙinsa Ɗan Anace, Shago ya yi nasarar doke (ko "kashe" adadin 'yan dambe) sama ɗari Uku da Talatin da Hudu (334) a tsawon rayuwarsa ta dambe.
Shaharar Shago tana da alaƙa ta kut-da-kut da mawaƙi Muhammadu Ɗan Anace, wanda shi ne makiɗin damben da ya fi kowa shahara. Waƙar da Ɗan Anace ya yi wa Shago tana ɗaya daga cikin manyan waƙoƙin damben gargajiya da ake saurara har yau.
Shago ya fito ne daga Maradun (wanda aka fi sani da Shagon Mafara) a jihar Zamfara, kuma dambensa ya zama abin misali ga dukkan masu son shiga harkar damben gargajiya.
A yau, akwai wasu 'ƴan damben na zamani da suka gaji sunan ko kuma suka fito daga zuri'arsa ko tsarin dambensa, kamar su Mustaphan Ɗan Shago da Ɗan Aliyu na Ɗan Shago, waɗanda ke fafatawa a filayen dambe na zamani a wurare kamar Kano, Kaduna, da Abuja. Shago ya rasu a ranar 3 ga watan Nuwamba1988.
Kafin ya mutu ya bar Dambe ya koma sana'ar dillancin shanu, kuma har ya koma ga Allah, Sarkin Musulmi Sir Abubakar III yana cigaba da tallafa masa tare da iyalinsa.
