Manya da kananan ‘yan siyasa, daga gwamnoni zuwa sanatoci da ‘yan majalisar tarayya da na jihohi na jam’iyyun adawa na ta tururuwar komawa cikin ta, lamarin da ya kai ga wasu ‘yan siyasa na fargabar cewa kasar na neman komawa tsari na jam’iyya daya tilo.
Sai dai wasu sun nuna cewa duk ƙarfin da APC take da shi a yanzu, a baya PDP ma ta yi irin ƙarfin, ta tumɓatsa kafin ta fara fashewa, har ta kai matsayin da take a yanzu na rashin tabbasi.
Duk da cewa PDP ce ta zo ta biyu a babban zaben kasar na 2023, amma ya zuwa yanzu ta yi asarar wasu daga cikin jigoginta, kamar dan takararta na shugaban kasa Atiku Abubakar, da wanda ya mara masa baya a takarar, Ifeanyi Okowa, inda suka sauya sheka.
Ya za a kwatanta karfi da tumbatsar PDP a lokacin ganiyarta da kuma APC wadda ke tata ganiyar a yanzu?