Narendra Modi ya samu tarba mai cike da girmamawa a Tel Aviv daga takwaransa na Isra’ila, Benjamin Netanyahu, tare da matarsa, Sara Netanyahu, yayin da ya isa ƙasar domin wata muhimmiyar ziyara ta aiki.
Ana sa ran shugabannin biyu za su tattauna kan shirin da Netanyahu ya gabatar na “tsarin kawancen kasashe shida” (hexagon of alliances), wanda ke da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe abokan hulɗa a fannoni daban-daban na tsaro, tattalin arziki da fasaha.Hankulan duniya sun karkata zuwa Isra’ila yayin da Firayim Minista Modi ke gudanar da ziyara ta biyu a ƙasar, bayan wadda ya kai a shekarar 2017. Ana sa ran wannan ziyara za ta ƙara zurfafa dangantakar da ke tsakanin Indiya da Isra’ila, inda batutuwan kasuwanci, tsaro da kuma fasahar ƙere-ƙere ta basirar wucin-gadi (AI) za su kasance a kan teburin tattaunawa.
Har ila yau, ana sa ran Modi zai yi jawabi a gaban majalisar dokokin Isra’ila, wato Knesset, wani mataki da ake kallonsa a matsayin alamar muhimmancin dangantakar da ke ƙara ƙarfi tsakanin New Delhi da Tel Aviv.