Majalisar wakilan Amurka ta amince da wani ƙuduri wanda zai dakatar da dukkan wani tallafi da Amurka take bai wa Najeriya har sai ƙasar ta ɗauki matakan daƙile matsalolin tsaro da ake fama da su a ƙasar.
A baya ƙudurin ya bai wa Amurka damar riƙe kashi 50% ne na tallafin, amma a yanzu majalisar ta ƙara shi zuwa kashi 100%.Ɗan majalisa Gregory Stuebe mai wakiltar gunduma ta 17 a majalisar wakilan Amurka daga jihar Florida ne ya gabatar da batun a zauren majalisar ranar Laraba.
Ɗan majalisar wanda ya wallafa bidiyon yadda aka tattauna kan ƙudurin a shafinsa na X, ya ce: "An amince da gyaran da na gabatar kan ƙudurin da ke neman Amurka ta daina bai wa Najeriya tallafi har sai gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakan hana yanka Kiristoci.