'YAN BINDIGA SUN KASHE SHUGABAN MASU SA-KAI A MALUMFASHI

 Katsina – Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe shugaban ƙungiyar masu sa-kai, Alhaji Nuhu Barau, yayin wani hari da suka kai ƙauyen Gora da ke Ƙaramar Hukumar Malumfashi a Jihar Katsina. Lamarin ya haddasa zanga-zanga da ta janyo rufe babbar hanyar Malumfashi zuwa Katsina na tsawon wasu sa'o'i.

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar, DSP Abubakar Sadiq, ya fitar a ranar Alhamis.

A cewar rundunar, da misalin ƙarfe 10:00 na safe a ranar Laraba ne Hedikwatar 'Yan Sandan Malumfashi ta samu kiran gaggawa cewa wasu 'yan bindiga masu ɗauke da makamai sun kai hari ƙauyen Gora.

Sanarwar ta ce nan take DPO na Malumfashi ya jagoranci tawagar jami'an tsaro zuwa wurin, inda suka yi nasarar fatattakar maharan tare da dakile harin.

Sai dai kafin isowar jami'an tsaron, maharan sun harbe tare da kashe shugaban masu sa-kai na yankin, Alhaji Nuhu Barau.

Rundunar ta ce daga baya wasu fusatattun matasa sun tare wani sashe na babbar hanyar Malumfashi zuwa Katsina, lamarin da ya katse zirga-zirgar ababen hawa na wasu sa'o'i. Jami'an 'yan sanda tare da sojoji sun isa wurin, suka shawo kan lamarin, suka buɗe hanyar tare da tarwatsa masu zanga-zangar.

DSP Abubakar Sadiq ya ce rundunar tana jajanta wa al'ummar yankin, tare da jaddada aniyar ta na kare rayuka da dukiyoyi. Ya kuma yi kira ga jama'a da su guji ɗaukar doka a hannunsu, su bi hanyoyin da suka dace wajen gabatar da ƙorafe-ƙorafensu.

A halin da ake ciki, wasu majiyoyin yankin sun ce harin ya kuma yi sanadin mutuwar wani mazaunin ƙauyen Gidan Barau, kuma masu zanga-zangar sun rufe babbar hanyar na kusan awa huɗu kafin jami'an tsaro su tarwatsa su.

Sai dai rundunar 'yan sanda ta tabbatar a hukumance da mutuwar Alhaji Nuhu Barau kaɗai, tana mai cewa bincike kan lamarin na ci gaba domin cafke maharan da suka tsere.

Post a Comment

Previous Post Next Post