"Auren Mutu'a Ya Zama Ijma'i Ga Malamai Da Wasu Malaman Sunna" Farfesa Ibrahim Ahmad Makari

An hango babban Limamin masallacin Ƙasa na Abuja, Sheikh Farfesa Ibrahim Ahmad Maƙari, a wani faifan bidiyo na karatunsa na yammaci da ya karaɗe soshal midiya yana bayani dangane da auren Mutu'a da kuma auren Mu'aƙƙad.

A ƙoƙarinsa na bayar da amsa (Fatawa) ga tambayar wasu bayin Allah da suka yi, waɗanda suke yawan tafiye-tafiye kuma matansu sun hana su ƙara aure, shi ne suka nemi fatawa a wurinsa, shin suna iya yin aure na wani ƙayyadajjen lokaci? 

Da farko malamin ya ba su amsa da cewa eh, za su iya yi. Sai daga baya ya zo da sharhi haɗi da tambihi dangane da ma'anar auren mutu'a inda ya ce:

"Mutu'a shi ne, namiji da mace za su iya su ce to, za mu yi aure iya na daren yau, su yi agreement aure za mu yi na daren yau kaɗai, ya ba ta sadaki shi ke nan ya aure ta."

Malamin ya ƙara da cewa, wannan a wajan malaman Shi'a ya halatta, da wasu ma ɗaiɗaiku daga cikin malaman sunna. Duk da ya zama ijma'i.

Malamin ya sake komawa baya a kalamansa, sannan kuma ya tabbatar da cewa, babu shi a sunna ga yadda ya faɗa a kalaman inda ya ce: "Sai dai a cikin malaman Sunna babu. Amma gaskiya akwai malaman sunnar da suka tafi a kanshi sosai da gaske a baya." 

Waɗannan na daga cikin malaman da suka jefa al'umma da yawa cikin ruɗani, tare da tambayar wai me Farfesa yake son ya faɗi ne a nan?

Farfesa Makari ya ƙara fito da bayani a fili, musamman lokacin da ya yi ƙoƙarin bambance tsakanin aure mu'aƙƙad wato ma'ana aure na wani lokaci na musamman da kuma auren mutu'a, wanda shi ma auren lokaci yake nufi. A ƙoƙarin bambance a baya ya bayyana ma'anar auren Mutu'a, yanzu kuma game da auren Mu'aƙƙad ga yadda Farfesa ya ce: "Shi Mu'aƙƙad, To amma idan ango a ransa bai sanya sharaɗi ba a lokacin, sai dai niyyarsa auren na kwana biyu ne ko na sati biyu ne, misali, a niyyarsa, sai dai ba a sa a cikin sigar ba, cewa za a yi auren kwana kaza. Shi ne kawai bambancin."

A taƙaice Malam yana son ya nuna cewa, mutum zai iya yin aure na wani lokaci (Mu'aƙƙad,) wanda ba a bayyana adadin kwanaki ko lokacin da za a zauna da matar da za a zauna na, sai da shi angon ya san cewa, auren da zai yi na ɗan wani lokaci ne, ba dawwamamme ba ne. To malam irin wannan auren ne ya halatta. Musamman ga mutanen da suke tafiya ƙasashen waje ko ma waɗanda suke yawaita tafiye-tafiye.

Post a Comment

Previous Post Next Post