Hukumar KASSAROTA Ta Fitar Da Wasu Sabbin Tsare-Tsare Da Suka Shafi Ayyukanta

​Hukumar KASSAROTA (Katsina State Safety and Road Traffic AuthorityHukumar Kiyaye Haɗurra da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Katsina ta fitar da wani muhimmin saƙo daga Sakataren Hukumar na jiha, Malam Aminu Lawal Batsari guda tara (9) domin ci gaba da inganta ayyukan hukumar da kuma kare lafiya da dukiyoyin al'umma. 

1. An hana Jami'in KASSAROTA aiki a hanya da sanda ko wani makami.

2. An hana bin wani da gudu, a kan abin hawa, don son kama shi.

3. An hana kama mutane dattawa masu yawan shekaru, in ba wani babban laifi suka aikata ba.

4. An hana tare mai abin hawa da ya ɗauko yara 'yan makaranta, in ba wani babban laifi ya aikata ba.

5. An hana tare jami'an da ke ayyukan agaji a hanyarsu ta zuwa aiki, kamar malaman lafiya da sauransu, in ba wani babban laifi suka aikata ba.

6. An hana tare magidanci da yake ɗauke da iyalinshi in ba wani babban laifi ya aikata ba.

7. An hana kame don lasisin tuƙa babur da aka daɗe ana kuka da ita.

8. An magance zabgawa mutane tara ba bisa ƙa'ida ba.

9. An hana cin mutuncin jami'an kassarota tare da tsattsauran mataki ga wanda ya aikata.

Kofar hukumar Kassarota a buɗe take kowane lokaci, ga duk wanda ke da sahihin ƙorafi domin sauraro.



Post a Comment

Previous Post Next Post