Za a yi wa fitacciyar jarumar shirin ‘BBNaija’ tiyatar rage girman mama
Fitacciyar tsohuwar ’yar takarar shirin Big Brother Naija (BBNaija), Dorathy Bachor, ta ce za ta yi tiyatar rage girman nono a shekarar 2027.
Dorathy ta bayyana hakan ne a shafinta na X ranar Laraba, inda ta ce ta je ganawa da likitoci domin tuntuɓarsu kan tiyatar, bayan shafe shekaru uku tana jinkirta ɗaukar matakin.
Ta ce a yanzu ta shawo kan fargabar da take ji, inda ta bayyana cewa shekarar 2027 za ta zama sabon babi a rayuwarta, da za ta aiwatar da birninta da tsoro yake shiga tsakaninsu.
Dorathy ita ce ta zo ta biyu a gasar BBNaija karo na biyar, wadda Laycon ya lashe.
A baya, jarumar ta bayyana cewa ta fuskanci matsananciyar fargaba da damuwa bayan kammala shirin, inda ta ce ta shafe shekara guda cikin yanayin rashin sanin abin da zai biyo baya a rayuwarta.